Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: An kai hari kan cibiyar al'adu ta musulmanTurkiyya da ke Montreal-Lacloux kuma an sami harsashi a cikin akwatin gidan waya. Majalisar Musulmi da kungiyar al'adu ta yi Allah wadai da hare-haren kuma sun yi gargadin cewa akwai karuwar kyamar Musulmi a Faransa.
Majalisar Musulmin Faransa ta bayar da rahoton sabbin ayyuka biyu na kyamar Musulunci a kasar. A wani masallaci da ke birnin Le Poy-en-Vela, wani mutum da ba a san ko waye ba ya yaga kwafin Alqur'ani da dama ya jefar a kasa, wani aiki da majalisar ta bayyana a matsayin "mummunan cin Zarafin Musulunci".
Your Comment